Yau kuma arangama ce tsakanin Gwamnan Bauchi da ƴan sanda
Автор: Madubi TV
Загружено: 2025-11-18
Просмотров: 23000
Описание: Tashin hankali ya ɓarke a yau a harabar sakatariyar PDP (Wadata Plaza) da ke Abuja, bayan da jami’an tsaro suka tare Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, daga shiga wajen. Lamarin ya haddasa zafafan saɓani tsakanin magoya bayan gwamnan da jami’an ‘yan sanda da DSS, inda aka yi wa taron cikas tare da sakin hayaki mai sa hawaye don tarwatsa cunkoso. Duk da cewa ba a samu rauni ko barna ba, yanayin ya kasance cike da hayaniya, tashin hankali da nuna ɓacin rai yayin da motocin gwamnan suka tsaya cak a ƙofar shiga. Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce daga bangarori daban-daban game da dalilin tsarewar da kuma abin da ya biyo baya.
Повторяем попытку...
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео
-
Информация по загрузке: