Gaba Dai Gaba Dai Niger 🇳🇪🇳🇪 Niger Sabouwa, Kadan Daga Ayyukan Cigaba Dakuma Tarin Kasar Niger
Автор: FRESH AREWA TV
Загружено: 2023-07-09
Просмотров: 9740
Описание:
Tarihin Jamhuriyar Nijar 🇳🇪
Jamhuriyar Nijar ta samo sunan ta ne daga kogin Naija (Niger) da ya dauko asali tun daga kasar Guinea zuwa Mali, Niger, Benin ya kuma ratsa Nigeria.
Nijar na makwabtaka da Najeriya da Benin ta kudanci, Burkina Faso da Mali ta yammaci, Aljeriya da Libiya ta arewaci, sai kasar Chadi ta bangaren gabas.
Kodayake sai a cikin karni na goma sha tara ne Turawa kamar Mungo Park dan kasar Burtaniya, suka fara shiga can bangaren kogin Naija, to amma dai tun kafin wannan lokacin Faransa ke ta kokarin ganin ta mallaki Nijar, inda ta samu nasara a shekarar 1890.
A wannan lokaci Faransa ta na da gwamnonin dake tafiyar da harkokin dukkanin yankunan da ta mamaye a yammacin Afirka ciki harda Nijar, wadanda ke aiki karkashin babban gwamna, wanda ke zaune a Dakar na kasar Senegal.
Tun dai lokacin babban birnin Nijar yana Zinder wato Damagaram har zuwa 1926 yayin da turawa suka mayar da shi a birnin Niamey.
Ranar goma sha takwas ga watan Disambar shekarar 1958, Niger ta zamo Jumhuriya mai cin gashin kanta a karkashin ikon Faransa.
Sannan a ranar uku ga watan Agusta na 1960, jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin kai, wato shekaru sittin da uku da suka wuce.
Jamhuriyar Nijar ta yi fama da juyin mulki daga sojoji daban daban wadanda suka mamaye madafen iko a kasar bayan ta samu 'yancin kai.
Babban abin da take fitarwa dai shi ne ma'adanin Uranium, bayan noma da kiwo da suke taka rawal azo a gani fannin tattalin arzikin kasar.
Amma a gefe guda kasar na hako man fetur wanda ke bunkasa tattalin arzikinta a yanzu.
Ana fitar kuma a tace ganga 20.000, zuwa karshen shekara ta 2023 Niger zata fitar da danyen mai ganga 100.000 a wuni.
Sunan kasar :Jamhuriyar Nijar🇳🇪
Adadin jama'a: Miliyan 26 ( 2023)
Babban Birni: NIAMEY
(Zinder, Maradi, Tahoua)
Manyan harsuna: Faranshi (na gwamnati), Larabci, Hausa, Songhai, Fulfude, Kanuri...
Addinai: Islam (%99), Kiristanci (1%)
Kudi : CFA (XOF)
Abubuwan da tafi fitarwa: Uranium, kayan noma, zinare...
Lambar waya ta kasa da kasa: +227
Shugaban kasa : Bazoum Mohammed
Shugaban gwamnati : Ouhoumoudou Mahamadou
Shugaban Majalisa : Seyni Oumarou
Повторяем попытку...
Доступные форматы для скачивания:
Скачать видео
-
Информация по загрузке: